Abdullahi Abbas

Rundunar ‘yan Sanda ta jihar Kano, ta gayyaci sabon Kwamishinan ma’aikatar ayyuka na musamman na jihar, Abdullahi Abbas, domin ya amsa tambayoyi kan maganganun da aka jiyoshi yayi a wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, yana kiran a yiwa Kwankwaso jifan Shaidan.

A cikin bidiyo, wanda ya yadu sosai, Abdullahi Abbas, anjishi yana yin kira ga magoya bayansu, da su yiwa “Shaidanin Siyasa” jifa, yana nufin tsohon Gwamna Kwankwaso, wanda ya shirya zuwa Kano a karshen watan nan.

Da yake shaidawa manema labarai ranar litinin a birnin Kano, Kakakin rundunar ‘yan Sanda ta jihar, Magaji Musa Majiya, rundunar na tsare da biyu daga cikin ‘ya ‘yan Abdullahi Abbas, da kuma wani yaron gidansa, akan farmakin da aka kaiwa ‘yan Kwankwasiyya a wajen daurin aure a jiya Lahadi.

Kamar yadda rundunar ta sanar, ta gayyaci Abdullahi Abbas ne sakamakon korafin da ta samu daga MK Umar and Co. inda suke kiran da a binciki maganganun da Abdullahi Abbas yayi, inda suka ce, yana neman efa jihar Kano cikin rudani da tashin hankali.

Ya kara da cewar, Abdullahi Abbas, tsohon Shugaban jam’iyyar APC tsagin Gandujiyya, an bayar da belinsa, sannan rundunar, na jiran masu karar Abdullahi Abbas da su gabatar mata da bidiyo din da suke zargin Abdullahi Abbas yayi kalaman da zasu janyo tashin hankali a jihar.

Haka kuma Rundunar ta bakin Magaji Majiya, tace, tana tsare da ‘ya ‘yan Abdullahi Abbas guda biyu da kuma mai yi masa aiki a gida, Sani Abdullahi da Abbas Abdullahi da kuma Nazifi Shawuya, akan zarginsu da hannu wajen jikkata wasu ‘yan Kwankwasiyya da suka je daurin aure a unguwar Chiranchi.

Yace, mun samu koke daga wani da yake cewar, yaran Abdullahi Abbas din suna da hannu wajen kaiwa ‘yan Kwankwasiyya hari a wajen daurin aure. Mun garzaya da su Asibiti a lokacin da abin ya auku domin basu kulawar gaggawa.

“Mun ci nasarar cafke kugun wadan da muke zargin, duk da cewar ana nan ana gudanarda bincike, idan har an same su da laifi, to, za’a gurfanar da su a gaban kotun Shari’ah”

Majaiya ya cigaba da cewar, yana mai yin gargadi akan masu shigar da sunan Kwamishinan ‘yan sanda cikin harkokin Siyasar jihar Kano. Yace aikin Kwamishi bai shafi siyasar kowa ba, aikinsa bai wuce tabbatar da gaskiya da adalci da kuma kokarin samar da zaman lafiya tsakanin al’umma ba.

LEAVE A REPLY