Daga Hassan Y.A. Malik

Kwamitin ladabtarwa ta jami’ar Islamiyya ta kasar Uganda (Islamic University in Uganda, IUU) da ke da matsuguninta a unguwar Mbale ta kori dalibai 23 da ke nazartar fannoni daban-daban da ta kama dalaifin aikta lalata a cikin jami’ar, laifin da ya saba da dokar gudanarwar jami’ar.

Kodinatan makarantar wanda kuma shi ne sakataren kwamitin ladabtarwar jami’ar, Dakta Sulait Kabali ya bayyanawa kafar yada labaraai ta Daily Monitor a jiya Litinin cewa an samu daliban su 23 da karya dokar makaranta wanda dokar ta tabbatar da kora ga duk wanda aka samu da aikata wannan laifi.

“An samu daliban da laifin aikata jima’i a tsakaninsu wanda hakan ya ci karo da dokar makaranta,” Dakta Kabali ya ce.

Dakta Kabali ya kara da cewa, an samu wasu daliban da laifin sata, shan barasa da wasu miyagun kwayoyi, wasu dalibai mata marasa aure an same su dauke da juna biyu da dai sauran laifuka.

Takardar korar daliban mai dauke da kwanan wata: 14 ga watan Afrilu, 2018 ta bayyana cewa an kama daliban na aikata jima’i a labe a lunguna daban-daban na makarantar kuma a lokuta daban-daban.

“A yayin tattaunawa da kwamitin ladabtarwa ta makaranta, daliban sun amince cewa an kama su turmi da tabarya a cikin duhu kuma a labe a lunguna suna aikata lalata a tsakaninsu.”

Dakata Kabali ya ci gaba da cewa, matakin korar zai zama jan kunne ga sauran daliban da ke da tunanin aikata irin wannan dabi’ar banzar a farfajiyar jami’ar.

Cikin daliban da aka sallama har da wadanda ke ajin karshe na kammala digirinsu, duk kuwa da cewa an baiwa daliban damar rubuta takardar koke ga hukumar jami’ar in har suna ganin cewa kwamitin ladabtarwa bai yi musu adalci ba.

Kakakin hukumar makarantar, Madam Rehema Katono ta ce makarantar na bin tsarin shari’ar musulunci ne, wannan ne ma ya sanya ta rubuta baro-baro a kundin dokar makarantar cewa duk dalibin da ya samu dalibar da ta yi masa kuma ya ke ganin sun fahimci juna, to, ya sanar da hukumar makaranta don ta tsaya masa a daura musu aure ta yadda za su samu ‘yancin tarawa a matsayin miji da mata.

Amma ko miji da mata, jami’a ba ta sahale musu runguma ko sumbatar junansu a bainar jama’a ba, kuma ba a yarda wani namiji ya zauna da mace daliba a harabar makaranta na tsawon minti 10 ba.

“Ba a bari mu zauna da dalibai maza na tsawon wani lokaci, kodayaushe ana saka mana ido,” a cewar wata daliba da ta bukaci da a sakaya sunanta.

LEAVE A REPLY