Daga Hassan Y.A. Malik

Wani mutum mai shekaru 50 da haihuwa da jami’an tsaro suka cafke bisa laifin dirkawa ‘yarsa ta cikinsa juna biyu ya magantu kan dalilin da ya sanya ya aikata wannan mugun aika-aika kuma ga ‘yarsa ta cikinsa.

Mutumin mai suna Taiwo Oyelabi da ke zaune a unguwar Iba, a gida mai lamba 15 da ke kan titin Community, daura da Obadore, ya fada komar ‘yan sandan jihar Legas bayan samunsa da laifin biyo dare tare da dirkawa ‘yarsa, Taiwo Nibilia Oyelabi, wacce ‘yar tagwaye ce.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Edgal Imohimi, a jiya Litinin, a lokacin da ya ke holin mai lafin  a shedikwatar ‘yan sanda ta jihar, ya bayyanawa manema labarai cewa sun samu rahoton kes din ne a ranar 16 ga wannan wata na Afrilu.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa, wannan lamari dai ya faru ne tun a watan Nuwamban shekarar 2017, a lokacin da Nibilia da ke zama tare da ‘yar uwar mahaifinta ta dawo wajen mahaifinta da zama, bayan da shi mahaifin ya matsa sai ‘yar tasa ta dawo gidansa da zama.

Tun daga wancan lokaci ne fa Taiwo ya ci gaba da yin mu’amalar aure da ‘yar tasa, dalilin da ya haifar da samuwar juna biyu.

Bincike dai ya nuna cewa  Taiwo mai gadi  ne, amma ko da wajen aikin dare za shi sai ya tafi da ‘yar tasa, lamarin da ya haifar da zargi, ya kuma sanya al’ummar unguwa suka dauki matakin yin kararsa ga ‘yan sanda.

Mista Taiwo ya bayyana dalilin aikata laifin ga kuma ‘yarsa ta cikinsa, inda ya bayyana hakan da cewa ‘yar tasa ce ta ja ra’ayinsa ta hanyar yin abubuwan da suke motsa sha’awarsa.

Taiwo ya bayyana ‘yarsa a matsayin wacce ke da shafar aljanu kuma sune suka ingizata wata rana yana zaune a daki kawai sai ta shigo ta rungume shi kuma ta fara sumbatarsa babu kakkautawa.

“Bayan mun gama kwanciya a wannan rana ne na yi mata dukan tsiya na kuma kaita mujami’a, inda a nan ne aka tabbatar min da cewa tana da aljanu.”

“Mun ci gaba da samun mu’amalar aure, mun yi ya kai kamar sau biyar kafin na fahimci cewa tana dauke da juna biyu.”

“Wannan aikin shaidan ne, yanzu ga shi ban san yadda zan yi da dan ba.”

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce da zarar ‘yan sanda sun kammala bincike za su tasa keyar Taiwo gaba kuliya.

LEAVE A REPLY