Daga Hassan Y.A. Malik

Sai da wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da sanata mai wakiltar Legas ta yamma, Sanata Solomon Olamilekan wanda ke tsaye a gaban fadar majalisar kafin daga baya kuma a sace sandar majalisar a jiya Laraba.

Sanata Olamilekan da aka fi sani da Yayi na tsaye ne a gaban ginin majalisar tarayyar Nijeriya a lokacin da ‘yan bindigar suka shigo farfajiyar majalisar suka jefa shi a cikin motarsu, sai dai Sanata Olamilekan ya tsere daga hannun ‘yan bindigar tun a jiyan.

Hadimin Sanata Olamilekan ya bayyana cewa, sace maigidansa ba zai rasa nasaba da kiran da ya yi a ranar Talata da a kori kafatanin shugabannin rassan tsaro na kasar nan.

“Jiya (Talata) a zauren majalisa, Sanata Olamilekan ya yi kira da gwamnati da ta kori shugabannin rassan tsaro na kasar nan a lokacin da ya ke bada gudunmawarsa game da kashe-kashen da wasu mutane da a ba a san ko su wane ne ba suka yi a jihar Nassarawa.

“Yau (Laraba), sai ga shi an sace Sanatan a gaban ginin majalisa kafin daga baya a zo a sace sandar majalisa. Sace Sanatan aka yi ba yunkurin sace shi aka yi kamar yadda wasu suke fada.

“Bayan dauke shi sun dauki hanyar fadar majalisar wakilai a kokarinsu na ficewa da shi daga farfajiyar ta wata kofa ta fita daga fadar gwamnati ta Aso Villa, kafin ya yi kukan kura ya kwace daga rikon da suka yi masa ya kuma yi tsalle ya diro daga motar, lamarin da ya sanya har zuwa yanzu ya ke dingishi,” a cewar hadimin sanatan.

 Sanatan na samun sauki.

LEAVE A REPLY