Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar
Daga Hassan Y.A. Malik
Rundunar ‘yan sanda jihar Jigawa ta shiga bincike ka’in da na’in kan dalilin da ya sanya wata budurwa mai shekaru 17 da haihuwa ta sha ruwan gubar nan da aka fi sani da Fiya-fiya.

Kakakin rundunar, SP Abdu Jinjiri ne ya bayyana hakan jiya a garin Dutse, babban birnin jihar ta Jigawa, inda ya ce lamarin dai ya faru ne a kaama hukumar Birni Kudu.

Labarin da ke iske mu shi ne na cewa, yarinyar mai suna Gambo Jibin mai shekaru 17 da haihuwa kuma ‘ya asalin kauyen Gambara, an kawo ta ne anga-ranga zuwa babban asibiti na Dutse bayan ta sha gubar.

An tura masu bincike su don su gano dalilin da ya saka Gambo ta aikata wannan danyen aiki a kan kanta, amma sai dai kafin su isa asibitin ta ce ga garinku nan.

Tuni dai aka mika gawar Gambo ga iyayenta don su yi mata sutura kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Kakakin ‘yan sanda ya ci gaa da cewa, tuni dai ‘yan sanda sun shiga aikin gano dalilin da ya sanya Gambo ta kashe kanta.

LEAVE A REPLY