Gwamnan jihar binuwai, Samuel Ortom

Majalisar zartarwa ta jihar Binuwai a ranar laraba ta amince da akashe zunzurutun kudi har Naira biliyan 8.3 domin gina hanyoyi a cikin manyan garuruwan jihar guda hudu.

A cewar kwamishinan yada labarai na jihar, Lawrence Onja, majalisar a zaman da ta yi a birnin Makurdi, ta kuma amince da kashe Naira biliyan 4 domin gina hanyar Awajir-Oju.

Mista Onojo, a lokacin da yake shaidawa ‘yan jarida bayan kammala zaman majalisar zartarwar jihar, ya zayyno hanyoyin da wannan aikin zai shafa wanda suka hada da Makurdi da Gboko da Katsina-Ala da kuma Otukpo.

Yace aikin hanyoyin zai cinye kimanin kilomita 54, za ayi aikin karkashin ma’aikatar ayyuka da sufuri da makashi ta jihar.

Mista Onoji ya cigaba da cewar, majalisar ta kuma amince da nadin Sunday Edoh a matsayin Shugaban kwalejin ilimi dake Ojo a jihar.

NAN

LEAVE A REPLY