Hassan Y.A. Malik

Hukumar tattara haraji ta kasa, Federal Inland Revenue Services, FIRS, a jiya Talata, ta kaddamar da aikin fara rufe kamfanonin da suke kaucewa biyan haraji, inda ta yi dirar mikiya akan wasu kamfanoni masu darajar biliyoyin naira a jihohin Kano, Legas da Ribas.

Kamfanin African Textile Management Limited na daya daga cikin kamfanonin da suka fuskanci fushin hukumar ta FIRS a jihar Kano, domin kuwa kamfanin ya tara bashin harajin da ya kai Naira miliya dari da talatin, da dubu dari biyar da sittin da bakwai, da dari biyu da talatin da kobo tamanin da takwas (N130, 567, 230.88)

Sauran kamfanonin da suka fuskaci rufewa daga FIRS sun hada da: Dumma Company Limited da kan titin Taura, kusa da defot din NNPC, Hotoro, Kano, wanda suka tara bashin haraji na sama da naira miliyan 24. Dennis Auto Supply Limited sun kwanta akan harajin da adadinsa ya kai Naira miliyan 62 da doriya. Reshen kamfanin A.Y and B da ke Kano, sun kauce biyan harajin sama da Naira miliyan 29.

A birnin Fatakwal na jihar Rivers kuwa, kamfanonin Halden Nigeria Limited, da Steve Integrated Technical Services Limited da Oil Field Services, Engineering and Equipment Leasing da kuma Stemco Limited sun fuskanci garkamewa bayan da aka same su da tarin kudaden haraji da suka ki biya da suka kai: Naira miliyan 197.6 da Naira miliyan 297.4 da Naira miliyan 131.7 bisa tsarin yadda muka jero sunayen kamfanin a sama.

A Legas kuwa, FIRS ta rufe kamfanin Interior Specifics da MP Engineering Contractors da Swiss Trade Limited da laifin kin biyan haraji kamar haka: Naira miliyan 17.125 da Naira miliyan 79.324 da Naira miliyan 11.009.

Ko a ranar Litinin din da ta gabata ma sai da FIRS a jihar Legas ta rufe: Crown Realities da Mega Equities Limited da kuma Medplus da ke kan titin Saka Tinubu a Victoria Island da dimbin bashin haraji kamar haka: Naira miliyan 86.3 da Naira miliyan 144.9 da kuma Naira miliyan 43.115.

Hukumomi a FIRS sun bayyana cewa babu kamfanin da za a bude sai ya biya kudaden da ake binsa na haraji gaba daya.

LEAVE A REPLY