Mai neman takarar Gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP Malam Salihu Sagir Takai ya kaiwa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ziyara a gidansa dake babban birnin tarayya Abuja.

Wannan ne dai karon farko da aka hadu tsakanin Takai da Kwankwaso tun bayan da Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Rahotanni sun tabbatar da cewar Sanata Kwankwaso ne ya gayyaci Takai zuwa Abuja domin tattauna yadda PDP zata samu Nasara a zaben Gwamnan jihar Kano a 2019.

LEAVE A REPLY