Attahiru Bafarawa

Kimanin kungiyoyin matasa guda 20 ne daga Arewacin Najeriya suka nemi Alhajai Attahiru Bafarawa ya fito neman takarar Shugabancin kasarnan a shekarar 2019,kungiyoyin sun hada da na matasa da mata, inda suka sha alwashin sayawa Bafarawa takardun shiga zabe.

Matasa wadan da suka yi wata ganawa a Kaduna, karkashin wata kungiya mai suna ‘Bafarawa Initiative for Peace, Unity and Progress” Matasan kuma sun kuduri aniyar yin wani gangami na mutum miliyan biyu domin yin kira ga Bafarawa ya fito takarar Shugaban kasa.

Jagoran matasan, Alhaji Abdullahi Muazu ya bayyana cewa “Zamu yi gangamin miliyoyin matasa ‘yan Najeriya domin zuwa gidan Attahiru Bafarawa a Sakkwato domin yin kira a gareshi da ya ceci al’ummar kasarnan ya fito takarar Shugaban kasa”.

Kungiyar ta bayyana cewar, Bafarawa mutum ne mai mutunci da kima a idanun al’ummar kasarnan lungu da sako, bugu da kari kuma mutum ne mai matukar son zaman lafiya a tsakanin al’ummar kasarnan da kuma kungiyoyin addinai.

“Yankin Arewa maso yamma shi ne yankin da yake da kwararrun ‘yan siyasa da zasu iya yiwa Najeriya takarar Shugaban kasa, domin fidda A’i daga Rogo a halin da kasarnan take ciki” A cewarsa.

Da yake maida jawabi, tsohon kakakin Attahiru Bafarawa, Alhaji Yusuf Dingyadi ya bayyana cewar, mai gidan nasa zai yi duba na tsanaki akan bukatun matasan na neman ya fito neman takarar Shugabancin Najeriya.

“Bafarawa nan ba da jimawa ba zai bada amsa ga bukatun al’ummar Najeriya musamman matasan kasarnan, akan buktunsu da kuma neman da suke yi masa ya fito ya ceci al’ummar kasarnan” A cewar Yusuf Dingyadi.

LEAVE A REPLY