Fitacciyar kungiyar addinin Musulunci ta Najeriya wadda ke da rassa a kasashen Nijar da Kamaru ta yi kira ya mabiyanta da su zabi Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben Shugaban masa da za ai nan gaba a wata mainkamawa.

Wannan umarni ya fito ne ta hannun Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo wanda ya bayyana hakan a wata huduba da ya yi a Yola babban birnin jihar Adamawa yayin da shugabannin kungiyar suka hadu domin shaida daurin auren ‘ya ‘Yan Shugaban Izalar.

Jalal Arabi babban Sakatare a fadar Gwamnatin tarayya da kakakin fadar Gwamnati Garba Shehu da kuma Musa Daura su ne suka wakilci Shugaba Buhari a wajen daurin auren.

LEAVE A REPLY