Sanata Muhammad Adamu Bello

Sanata Muhammad Adamu Bello, daya daga  cikin manyan jam’iyyar PDP a jhar Kano, kuma daya daga cikin masu neman jam’iyyar ta sahale musu yin takarar Gwamnan Kano a zaben shekarar 2019. A wannan tattaunawa da yayi da jaridar Daily Nigerian, Sanata Muhammad Bello, wanda ya taba wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, a majalisa ta 6, yayi bayanai masu yawa a yain wannan tattaunawa, kan Gwamnatin Buhari da kuma batun takararsa ta Gwamnan Kano.

A yayin wannan tattaunawa, Sanata Muhammadu Bello ya bayyana cewar, jam’iyyar PDP na da kwarin guiwar cin zaben Gwamnan Kano dama na Shugaban kasa, matukar anyi abinda ya dace. Dole Shugabannin jam’iyya a mataki na kasa da ma jihohi su sanyawa al’umma ‘yan takarkaru masu nagarta wadan da jama’a suka yadda da da su kuma suka aminta da nagartarsu, daga bisani kuma abar sauran al’umma su yi alkalanci a ranar zabe.

Haka kuma, Sanata Muhammadu Adamu Bello yace, matukar PDP suka sanya dan takarar Shugaban kasar da ya dace, to babu shakka, zai iya kayar da Shugaba Buhari,indai aka kaucewa batun nan na dauki dora, ko kaci baka ciba, baka ciba kaci, to yanzu ‘yan Najeriya a sheirye suke su sake baiwa jam’iyyar PDP dama domin halin da ake ciki na tsananin yunwa yasa babu abinda al’umma suke nema ace mafita.

Haka kuma, a yayin tattaunawar, Sanata Muhammadu Bello yace, dole a yabawa Shugaba Buhari kan kokarinsa da dirkake ‘yan ta’addar Boko Haram, domin acewarsa a Maiduguri yayi karatun jami’ah, don haka duk abinda ya shafi Maiduguri ya shafe shi, kuma wannan abin a yaba ne yadda aka murkushe ‘yan kungiyar Boko Haram.

Ya kuma kara da cewar mafiya yawan alkawuran da jam’iyyarAPC ta yiwa ‘yan Najeriya bata iya cikawa ba, wannan kuma dalili ne da zai sanya ‘yan Najeriya zasu dawo daga rakiyarta, domin su sake baiwa PDP dama, domin ta karanci darasi akan kurakuran da ta yi a baya.

LEAVE A REPLY