Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa,Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewar a zaben 2019 da yake tafe, idan ‘yan Najeriya suka kayar da APC da Buhari tilas ne shima Buhari da APC su yarda da sakamakon zaben, kuma su karbi faduwa kamar yadda Goodluck Jonathan yayi a 2015.

Sule Lamido ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron tattaunawa kan batun zaben 2019 da kalubalen da suke tattare da zabe. Taron dai kamfanin Mediya Trust masu buga jaridar Daily Trust ne suka shirya shi a Abuja domin tattaunawa kan zaben 2019.

A yayin taron, Sule Lamido daga bangaren jam’iyyar PDP ya gabatar da dogon jawabi kan batun siyasar Najeriya da kuma irin abubuwan da jam’iyyar PDP tayi na bajinta game da zaben 2015 da ya gabata.

“Tilas ne a ramawa kura aniyarta a zaben 2019, idan PDP ta kayar da APC dole ne su karbi faduwa kamar yadda muka yi a baya”

Sai dai a nasa jawabin, Sakataren Gwamnatin tarayyar Najeriya Boss Mustapha, ya mayarwa da Sule Lamido martani, yace indai Sule Lamido ne zai yiwa PDP takara to ba makawa Buhari yaci zabensa karo na biyu.

Haka nan, shima Sanata Saidu Dansadau ya kalubalanci kalaman na Sule Lamido, inda yace duk abinda Sule Lamidon ya fada game da PDP ba gaskiya bane. “A babban taron PDP na shekarar 1998, ai Sule Lamido bai goyi bayan Obasanjo ba, ya goyi ayan Alex Ekwueme ne ya zama dan takarar PDP”

Tsohon Gwamnan jihar Legas, kuma jagoran jam’iyyar APC na kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu ne ya wakilci jam’iyyar APC a wajen wannan tattaunawa da aka yi domin duba yadda zaben 2019 zai kasance.

LEAVE A REPLY