Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki
Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya karyata rahotannin da suke nuna cewar zai nemi tsayawa takarar Shugaban kasa a shekarar 2019, yace “idan har ya yanke shawarar tsayawa takara, za’a ga rahotannin a manyan jaridun Najeriya”.
Wata jarida mai suna The Boss ita ce ta fara ruwaito cewar Mista Saraki zai yi takarar neman Shugabancin kasarnan a shekarar 2019 da za’a yi nan gaba.
“Wata majiya da ba tada tushen labarinta ta fara yada jita jitar cewar, Saraki na shirye shiryen kaddamar da neman takarar Shugaban kasa, yace idan har zai yi hakan, to sai ya tattauna da ‘yan Najeriya lungu da sako domin samun shawarwari”
Haka kuma, Jaridar Daily Independent ta ruwaito Yusuph Olaniyonu, babban mai taimakawa Saraki akan hulda da kafafen yada labarai yana cewar babu kanshin gaskiya a rahotannin da aka bayar na tsayawa takarar Saraki neman SHugabancin Najeriya.

LEAVE A REPLY