Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Mai taimakawa tsohonShugaban kasa Goodluck Jonathan akan harkokin yada labarai,Mista Reno Omokri ya tofa albarkacin bakinsa kan aniyar Shugaba Buhari ta yin tazarce a 2019.

Omokri wanda daya ne daga cikin fitattun masu adawa da salon mulkin Shugaba Buhari, ya bayyana yuwuwar sake zaben Buhari a 2019 da cewar kamar samun nasarar Gwamnan Kaduna Nasiru el-Rufai ce, wadda ke da matukar wahala.

A cewarsa, Shugaba Buhari ya mayar da ‘yan Najeriya sakarkaru, da yace zai sake neman wa’adin mulki karo na biyu, yace, har ya zuwa yanzu babu wani aiki kwaya daya kacal da Shugaba Buhari ya faro shi kuma ya kammala shi da za’a iya bugun gaba da shi.

Reno Omokri, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter “Mun ji dadi da Gwamna el-Rufai ne ya sanar da cewar Shugaba Buhari zai sake yin takara a zaben 2019, domin nasarar Buhari kamar nasarar el-Rufai ce wadda ke da kamar wuya.

“Mutumin da babu wani abu guda daya da zaka iya nunawa kace shi ne yayi shi aka samu nasarar kammalawa,kuma wai shi ne zai zo neman mulki karo na biyu” A cewar Reno Omokri a shafinsa na Twitter.

LEAVE A REPLY