Atiku Abubakar yayin da yake gabatar da jawabi a Chatham House a Landan

Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, a ranar Laraba ya gabatar da wani jawabi a ‘Chatham House’ a birnin Landan, inda ya bayyana kudurorinsa guda shida idan ‘yan Najeriya suka zabe shi ya zama Shugaban kasa a 2019.

Wazirin Adamawa ya bayyana cewar idan aka zabe shi a 2019, Gwamnatinsa zata tabbatar an samu bunkasar tattalin arziki ta hanyar bunkasa harkar jirgin kasa da kuma sake fasalta yadda tsarin Najeriya yake.

Kudurorinsa guda shida idan ya zama Shugaban kasa su ne:

  1. Samar da sabbin hanyoyin samrwa da Gwamnati kudade                              “Idan na zama Shugaban kasa zan sake sauya tsarin samarwa da Gwamnati kudaden shiga, zamu rage dogara da kudaden mai kadai domin samun kudin shiga, sannan kuma, zamu samarda dawwamammen tsarin gudanarwa a harkar Manfetur wadda ba tada garari da yawa a ciki.”

2. Fadada harkar sufurin jiragen kasa                                                                       “Zamu yi kokarin fadada harkar sufurin jiragen kasa, ta yadda zata sadar da ma’aikata da guraben aikinsu, ta sadar da dalibai da makarantunsu, sannan ta sadar da iyayen dake kauye da ‘ya ‘yansu dake rayuwa a cikin birane ba tare da wata matsala ba.”

3. Sake fasalta Najeriya                                                                                              “Na gamsu cewar lallai akwai bukatar sake fasalta yadda Najeriya take, ta yadda zamu baiwa kowwanne abu abinda ya dace ba tare da cutarwa ba. Zamu bunkasa harkar samarda kudaden haraji gwargwadon abinda ake da shi a ko ina, zamu inganta abubuwan da koina suke samarwa,da kuma batun samarda cikakkiyar walwala ga dukkan al;ummar Najeriya”

4. Kaddamar da yadda za’a daidaita abunda muke samu da abinda muke da shi    “Zan tabbatar da cewar an shaye dukkan wani kogi da yake bukatar hakan (Musamman a Arewacin Najeriya babu gabar teku) domin amfanin al’ummar dake kan hanyarsa dama sauran kasa baki daya. Zamu bayar da lasisi ga jihohi su fara sarrafa dukkan abinda suke da shi na daga albarkatun kasa.”

5. Zamu sanya jari mai yawa a harkar Ilimi                                                             “Zamu tabbatar da cewar, dan abinda muke samu na daga cikin kudaden shigar Gwamnati, mun sanya kudade masu yalwa a harkar Ilimi da kiwon lafiya, tare da cin tarar dukkan jihohin da suka bijirewa sanya abinda ya dace a wannan janibi. Dalibai miliyan daya da dubu dari shida (1.6m) suke rubuta jarabawar shiga jami’a, amma da kyar dubudu dari shida suke samun guraben karatu. Muna biyan sama da Dalar Amurka biliyan guda don yaranmu su yi karatu a Ghana.”

6. Kirkiro hanyoyin da zamu tabbatar da tsayayyen farashin kudaden musaya     “Ya zama wajibi mu samar da tsayayyen farashin kudaden musaya, ta yadda masu zuba jari zasu iya yin lissafi na shekaru masu yawa da kudaden da suke da shi ba tare da samun hawa da sauka na farashin kudaden musaya ba. Bana goyon bayan a dinga samun sauyin farashin kudaden musaya a ko da yaushe.”

LEAVE A REPLY