Shugaba Muhammadu Buhari

Dan majalisa zamanin jamhuriya ta biyu, Dakta Junaidu Mohammed, ya bayyana cewar ‘yan Najeriya zasu yi nadar sake zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari, matukar suka kuskura suka sake zabensa.

Shugaba Buhari a jiya Litinin ya bayyana aniyarsa ta sake neman wa’adin mulki na biyu a shekarar 2019, a wani taron sirri da ya gudana tsakanin gaggan jam’iyyar APC da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Junaidu Mohammed yace, ya rage na ‘yan najeriya ko dau su sake zabensa ko kuma kada su sake zabensa.

Da yake magana da Jaridar Vanguard, Junaidu Mohammed yace “Na san babu wani wanda zai yi mamaki da bayyana aniyarsa (Buhari) ta sake tsayawa zabe”

“Meye yasa? Saboda Buhari mutum ne da babu ruwansa da abinda ya shafi ‘yan Najeriya, kuma yana son dawwamar da kansa akan mulki a zatonsa”

“Yanzu dai shawara ta rage ga mai shiga rijiya, ‘yan najeriya su ne zasu yanke hukunci, ko dai su zabe shi (wanda jefa kansu cikin wahala ne) ko kuma su yi wancakali da shi”

“Abinda zan fada balo balo shi ne, Idan Buhari ya sake cin zabe kuwa, ba za’a taba kawo karshen cin hanci da rashawa ba, tabarbarewartsaro da ayyukan ‘yan ta’adda duk zasu cigaba”

 

 

LEAVE A REPLY