Barau Garba, Dansandan da ake zargi da yiwa Maryam fyade

Fatuhu Mustafa wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Najeiya, ya Wallafa a shafinsa na facebook, labarin wani Ɗansanda da ya yiwa wata yarinya mai kimanin shekaru 13 fyade a birnin warri na jihar Delta.

Yarinyar mai suna Maryam ance ‘yar asalin jihar Kano ce. Ɗansandan ance ya kulle yarinyar ne a dakinsa inda ya dinga saduwa da ita, kafin daga bisani dubunsa ta cika.

An bayyana sunan Ɗansandan da Barau Garba NFA 275601. Tuni dai wannan batu ya harzuka mutane da dama a shafukan sadar da zumunta na intane, inda da yawa suke Allah wadai da wannan aikin assha tare da kiran hukumomi su dauki mataki akan wannan Ɗansanda domin kwatowa wannan yarinya hakkinta.

Ku bayyana mana ra’ayinku kan wannan aikin assha da wannan Ɗansanda ya aikatawa wannan yarinya.

LEAVE A REPLY