Mambobin kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano, sun mamaye ofishin kamfanin MTN na jihar Kano, yayin da suke nuna rashin jin dadinsu kan yadda kamfanin ke nuna wariya yayin daukar ma’aikata na wucin-gadi.

Binciken DAILY NIGERIAN ya gano cewar kamfanin na sanya tsauraran sharudda ga ma’aikatansa kafin su kasance na din-din-din ta yadda ba’a iya samun wadan da suke iya cika sharuddan da kamfanin yake sanyawa.

“Wannan ba adalci bane, ya kamata duk ma’aikacin da za’a dauka ya zama na din-din-din ne ba irin yadda gaba daya ma’aikatan kamfanin suka zama na wucin-gadi ba, sam babu adalci a irin yadda kamfanin ya sanya sharuddan da ba’a iya cika su”

“A saboda haka kungiyar kwadago ta kasa ta yi kira ga ma’aikatar daukar ma’aikata da kuma ma’aikatar sadarwa ta kasa da su sanya baki akan abinda kamfanin MTN din yake yiwa ma’aikatansa a jihar Kano” A cewar Shugaban kungiyar kwadago ta asa reshen nihar Kano, Kabiru Ado Minjibir.

 

 

LEAVE A REPLY