Yadda aka kone barawon babur a Yawuri, jihar Kebbi

Wani da abin ya faru akan idonsa, Sani Bala Yawuri, ya wallafa a shafinsa na facebook cewar wasu matasa sun bankawa wani barawon babur wuta ya kone kurmus, inda ya kone nan take.

A cewarsa “Yan sanda sunyi kokarin kubutar da barawon babur din, amma jama’ar dake wajen sun sha karfin ‘yan sandan, dan haka ba abinda suka iya yi sai su kalli yadda mutane suke daukar doka a hannun su”

Wannan shi ne irin misalin yadda mutane ke daukar doka a hannunsu, suna zartarwa da mutane hukunci ba tare da zuwa wajen hukuma ba, hakan kuma ba alheri bane.

Muna fatan hukumomi zasu yi bincike domin kamo wadan da suke da hannu kan wannan al’amari.

LEAVE A REPLY