Sophia Mutum-mutumi tare da Amina Mohammed mataimakiyar sakataren majalisar dinkin duniya

Ƙasar Saudiyya ta zama kasa ta farko da ta baiwa mutum-mutumin nan mai suna Sophia Igama ko iznin zama dan asalin zama dan kasar. Wannan sanarwar ta zo ne bayan da aka gudanar da wani babban taron da ya shafi kasuwanci da zuba jari a babban birnin kasar Riyadh.

Sanarwar tace, an shaidawa mutum-mutumin cewar, “muna farin cikin shaida miki cewar, a halin yanzu mun baki tardun iznin zama ‘yar kasar Saudiyya” Mutum-mutumin mai suna Sophia tayi godiya ga kasar ta Saudiyya bisa wannan karamci da aka yi mata.

Sophia ta fada a bainar jama’a cewar, “ina matukar farin ciki da nuna jin dadina bisa wannan karramawa da yi min a kasar Saudiyya, abu ne mai cike da tarihi ae nice mutum-mutumi na farko da na samu irin wannan damar a Saudiyya”.

Ita dai Sophia Mutum-mutumi ce da aka kaddamar da ita a birnin Dubai yayin wani taron fasahar kere-kere ta duniya da aka gabatar a ‘yan kwanakin da suka gabata. Ana tattaunawa da wannan mutum-mutumi kuma ya bayar da amsa nan take.

“yan jarida daban daban daga kasashen  duniya ne suka yi hira da Sophia kuma ta basu amsa nan take. A yayin babban taron da aka yi a Dubai, itama mataimakiyar babban sakataren majalisar dinkin duniya Hajiya Amina Mohammed wadda ‘yar najeriya ce, tayi hira da wannan mutum-mutumi mai suna Sophia.

Me zaku ce kan wannan abin al-ajabi?

 

LEAVE A REPLY