Wasu ‘yan mata guda hudu ne suka nitse a ruwa a birnin Dutse na jihar Jigawa yayin da suke wanka a wani kududdufi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Abdu Jinjiri, ya tabbatar da hakan a lokacin da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar lahadi a birnin Dutse.

Mista Jinjiri, yace ‘yan matan da suka rasu mutanan kauyen Sakwaya ne, wani karamin kauye a karamar hukumar Dutse.

Ya bayyana sunayensu kamar haka: Sumayya Gadi ‘yar shekara 7 da Zuwaira Abdulhamidu ‘yar shekara 12 da Gaji Saidu ‘yar shekara 12 da Ummi Saidu ‘yar Shekara 11.

Yace ‘yan matan sun gamu da ajalinsu ne, a lokacin da suka nitse a cikin ruwa akan hanyarsu ta zuwa garin Farantawa dake yankin karamar hukumar Albasu domin yin itace.

Mista Jinjiri ya cigaba da cewa, ‘yan uwan mamatan ne suka sanar da rundunar ‘yan sandan jihar da misalin karfe 1:30 na rana bayan da suka samu nasarar tsamo gawarwakinsu daga ruwa.

Ya kara da cewar, wani karamin asibii dake yankin shi ne ya tabbatar da mutuwar ‘yan matan, kuma tuni aka yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Sannan daga karshe ya bukaci iyaye da su sanya idanu akan inda yaransu suke zuwa da kuma inda suke yin wasa, domin kaucewa sake aukuwar hakan anan gaba.

Sannan ya bukaci al’umma da su kai daaukin gaggawa a yayin da aka samu wani yana cikin mawuyacin halin da zai iaya halaka shi ba sai an jira hukuma ta zo ba.

NAN

LEAVE A REPLY