Sheikh Ahmad

Fitaccen Malamin addini dake Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi ya sake caccakar Shugaba Buhari. Shehun Malamin ya bayyana a ckin Tafsirinsa da yake gabatarwa a masallacin juma’a na tunawa da tsohon Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, ina ya bayyana cewar zubar da jinin da ake yi a wannan Gwamnatin ta Buhari yafi duk wanda aka yi a zamanin Gwamnatin Jonathan da ta gabata.

Da yake yin Tafsirin wannan shekarar na Ramadan, Shehun Malamin ya sha caccakar manufofin Gwamnatin Shugaba Buhari, inda a sau da dama yakan kamanta Gwamnatin da ta Jnathan da ta shude, wajen kashe kashe.

Idan za a iya tunawa a baya zamanin Gwamnatin Jonathan da hare haren Boko Haram suka yi kamari, Sheikh Ahmad Gumi yayi kira da kakkausar murya ga Jonathan da kada ya sake tsayawa neman zabe. Da yake gabatar da tafsirin, ya zo da kwafin jaridar New Nigerian ina ta buga kalamansa na kira ga Jonathan da kada ya tsaya zabe.

“Dalilin da ya sanya na caccaki Shugaba Jonathan saboda yadda muke ganin yana sakaci Boko Haram suna cin karensu babu babbaka, suna sanya bamabamai ko ina kuma gwamnatti bata yin ko in kula”

 

LEAVE A REPLY