Shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki

Kotun kolin tarayyar Najeriyata wanke shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki kan zargin da akai masa na kin bayyana kadarorin da ya mallaka a takardun cikewa domin shiga zabe.

Babban mai shariah na kotun kolin Joji Centus Nweze ya bayyana cewar Saraki ba shida wani laifi kan zarge zargen da kotun da’ar ma’aikata take yi masa na yin karya wajen bayyana kadarorin da ya mallaka a takardun cikewa don shiga zabe.

Haka kuma kotun ta yi watsi da wasu zargezarge da ake yiwa Saraki guda uku.

LEAVE A REPLY