'Yan gudun hijira yayin da suke komawa gidajensu a jihar Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara ta baiwa ‘yan gudun hijira tabbacin samun zaman lafiya a yankunansu, da haka ta umarce su da su koma gida, yayin da tace tsaro ya inganta a yankunan nasu.

Gwamnan jihar Zamfara AbdulAzeez Yari Abubakar ne ya bayar da wannan tabbacin, a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan da ya jagoranci wata tattaunawa ta musamman da majalisar tsaro ta jihar.

Gwamnan yace, sun dauki matakin tura isassun jami’an tsaro yankunan da ake fama da tashin hankali wadan da zasu baiwa al’umma kariya.

 

LEAVE A REPLY