Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku

Gwamnan jihar Taraba Darus Dickson Ishaku, yayi gargadi kan yunkurin kaiwa jiharsa mummunan hari nan da kwanaki goma, inda ya bayyana cewar ba shi da wani katabus kan batun sha’anin tsaron jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a birnin Jalingo, a lokacin da Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Yarima Uche Secondus ya kai masa ziyarar ta’aziyar hare haren da aka kai jihar a kwanakin baya wanda harin ya rutsa da dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar karamar hukumar Takum, Hosea Ibi.

Gwamna Ishaku ya bayyana cewar, jihar Taraba itama ta karbi kasonta na hare haren Fulani makiyaya tun farkon wannan shekarar, a cewarsa, al’amarin tsaro a jihar yayi mugun tabarbarewa kamar dai jihar Binuwai.

Gwamnan ya cigaba da cewar “Shugaban jam’iyyar PDP, wannan abin farinciki ne gareka a matsayinka na Shugaban majalisar koli ta jam’iyyarmu, ka zo kafa da kafa tun daga Habuja domin ka jajanta mana. Ya mai girma Shugabanmu, anan tare da mu, akwai dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar Taraba, nine na shaida musu cewar yau zaka ziyarce mu domin jajanta mana, tare da yi mana ta’aziyar dan majalisar da muka yi rashi”

“Ya mai girma Shugabanmu, ina son na shaida maka cewar,, babu ko tantama al’amuran tsaron sun yi mugun tabarbarewa, bai wuce awa guda tsakaninmu da Hon. Hosea Ibi, na samu kira daga abokin aikinsa cewar an yi garkuwa da shi, kuma a daura da bataliya ta 93 a barikin soji dake Takum, a lokacin yaje domin tattaunawa da mahaifiyarsa da kuma ‘yan uwansa”

“Ya mai girma Shugaban PDP, ina matukar jin zafi a matsayina na Gwamna, domin abinda na fara rantsewa akansa wanda na yiwa al’ummar jihar Taraa alkawari shi ne zan amintar da rayuwarsu da kuma dukiyoyinsu a duk inda suke, nace musu, su amince da zaman lafiya, ni kuma zan samar musu cigaba. Da na tambayi ‘yan taraba shin sunga wani abu na cigaba? Kuma suka amsa da eh sun gani”

“Ranka ya dade, yanzu fa ba wani batun samar da cigaba muke yi a jihar Taraba ba, batun da muke yi yanzu shi ne na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ina cikin jimamin wadan da suka kattaba kundin mulkinmu, inda muka yi alkawarin bayar da kariyar ta rayuwa da dukiya,amma abin kaico mun gaza”

“Mun kwaikwayi siyasarmu daga kasarAmurka, amma sai dai kash, mun kwaikwayesu ba yadda ya dace ba. Muna da ‘yan doka da matakin kananan hukumomi da jiha inda muke da manyan ‘yan sanda suna jibge ko ina a jihar, amma idan ka zaga ba abinda zaka gani sai sojoji cikin shigar yaki, suna zare mana idanu”

“Ni ne gwamnan jihar nan, amma abubuwa ne naman shan kaina, tayaya zan iya aikin da ya dace? ta ya zan iya tabbatar da mulkina? Ace ina nan tare da ‘yan sanda amma abubuwa suna gagararmu, amma dole idan muna son samun nutsuwa sai daia mu dogara ga jami’an tsaron Gwamnatin tarayya”

“Ya mai girma Shugabanmu, kamar yadda ka bayyana mana, abu mafi karanci da Gwamnati zata yi, shi ne ta baiwa jama’a aminci akan rayukansu da dukiyoyinsu, zaka sha mamaki kaji labarin cewar, mutum yaje gona, amma kafin ya dawo an farwa kauyensu an kashe iyalansa”

“A yanzu haka da nake yi muku magana, wasu mutane da har yanzu bamu san ko su waye ba, sun sha alwashin farwa jihar Taraba, ta hanyar kai mata mummunan hari nan da kwanaki 10masu zuwa, muna nan muna dakonsu. Muna fada ne yanzu sabida idanabin ya auku, wane zai iya cewar ai bamu fada ba”

“Ina fada ina kuna nanatawa, jirgin helkwafta yana yawo yana jibge makamai anan jihar Taraba, ya kamata hukumomi su san abin yi kafin lokaci ya kure mana”

LEAVE A REPLY