Sabon zababben Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus

Babban taron da jam’iyyar PDP ta gudanar a Abuja ya bar baya da ƙura, domin wasu da basu sami nasara a zaben ba, sun bukaci uwar jam’iyyar ta kasa da ta dawo musu da kudadensu na takardun shiga zaben da suka saya.

Tuni dai uwar jam’iyyar daman ta kafa kwamitin sulhu ga ‘ya ‘yan jam’iyyar karkashin Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson, domin sulhunta wanda suke ganin an bata musu ko an yi musu ba daidai ba. Haka kuma, Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan na ta yunkurin dannan kirjin wadan da suka fusata da sakamakon zaben.

Bayan haka, wasu wadan da basu yi nasara a zaben ba, sun yi korafin cewar wannan nadi ne aka yi maimakon zaben da tun farko aka ayyana cewar za’a gudanar. A lokacin da yake tattaunawa da sashin Hausa na BBC, Aliyu Manji, wanda yayi takarar mukamin mataimakin Shugaban jam’iyyar daga Arewa, yace sam zaben ba sahihi bane, dan haka ya bukaci a dawo masa da kudinsa.

“Wannan zaben sam ba a taki gaskiya a cikinsa ba, domin cike yake da rashin gaskiya. Babu wani abu da yayi kama da gaskiya a ciki, wasu ne kawai suka yi abinda suka saba na dauki dora, domin wasu ma ko takardun shiga zaben basu saya ba aka ce su ne suka ci zaben”

“Dan haka muna kira ga uwar jam’iyyar PDP ta kasa, kafin mu dauki mataki ya kamata su kiramu su dawo mana da kudadenmu da muka biya na shiga takarar” Inji Aliyu Manji.

Amma kuma, tsohon Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido yayi kira ga wadan da suka yi fushi da su yi hakuri komai zai warware cikin sauki. Sannan su karbi wannan sakamako da zuciya daya, domin zabe ne da aka yi shi a bainar jama’a.

“Mutanan da suke zargin anyi wasu abubuwa ba daidai ba a yayin wannan zabe, su sani fa, wadan da suka shirya wannan zabe, mutanene amintattu kuma masu mutunci a Najeriya, domin mafiya yawancinsu, ko dai tsofaffin Gwamnoni ne, ko kuma tsofaffin Ministoci, haka suma, lokacinsu, wasu sun fadi, su kuma suka yi nasara”

“A cikin jam’iyyar da take da mutanen irin wannan, ace mun iya shirya babban taro na kasa irin wannan kuma mun yi zabe lami lafiya, ai babba abin bugun kirji ne, kuma abin a yaba ne matuka” Sule Lamido na martani a BBC Hausa ga wadan da suka dauki zafi dangane da sakamakon zaben.

LEAVE A REPLY