An bayar da labarin a kalla fasinjoji 42 ne aka yi garkuwa da su akan hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna, mutanan ne dai suna kan hanyar su ne ta zuwa Kano, inda ‘yan ta’adda da suka addabi yankin na Birnin-Gwari suka sace su tare da yin garkuwa da su.

Shugaban kungiyar ‘yan yuniyal ta garin Birnin-Gwari shi ne ya shaidawa majiyar PRNigeria cewar a tsakanin yammacin ranar Talata zuwa wayewar garin Laraba aka sace mutanan akan hanyar Birnin-Gwari.

Shugaban yuniyal din da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewar “A tsakanin jiya zuwa safiyar nan ta Laraba aka sace mutanan a daidai kauyukan Kuriga da Kagara, inda aka dauke fasinjojin zuwa cikin daji aka yi garkuwa da su”

“Wasu daga cikin direbobin da suke bin hanyar ne da suka ci nasarar guduwa suka ga abinda ya faru kuma suka je suka shaidawa kungiyar ‘yan yuniyal ta garin Birnin-Gwari abinda ke faruwa a yankin.

PRNigeria ta ruwaito cewar tuni aka sanarda dukkan sassan jami’an tsaro abinda ke faruwa, kuma sun shiga aikin ceton mutanan da aka yi garkuwa da su ba tare da wani bata lokaci ba.

 

LEAVE A REPLY