Gwamnonin kano Ganduje, Oyo Ajimobi, Zamfara Yari sai kuma Sarkin Kano a tsakiya Muhammadu Sunusi

Gwamnan jihar Oyo Mista Abiodun Ajimobi tare da wata kakkarfar tawagar da ta kunshi Gwamnonin yankin kasashen Yarabawa da shugaban gwamnonin Najeriya Abdulaziz Yari Abubakar, Gwamnan Jihar Zamfara, sun zo Kano domin nemawa dan Gwamna Ajimobi auren ‘yar Ganduje.

Fatima Abdullahi Umar Ganduje, ‘yar gidan Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ana sa ran zata angwance da Isiyaka Abiodun Ajimobi, nan ba da jimawa ba.

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu ne ya karbi tawagar Gwamnonin a fadarsa, bisa jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Gwamnonin sun je fadarSarkin ne domin nemawa Issiyaka Ajimobi, dan gidan Gwamnan Oyo auren fatima Ganduje.

Ana sa ran dai nan ba da jimawa ba za ayi wannan kasaitaccen biki tsakanin Bahaushiyar ‘yar Kano da Kuma Beyerabe dan asalin kasar Oyo hedikwatar kasar Yarabawa a yankin kudu maso yammacin najeriya.

Wannan bikin dai ana ganin na daga cikin abin da zai dauki hankali sosai, kasancewa mahaifan ango da amarya dukkansu Gwamnoni, kuma daga kabilu daban daban.

LEAVE A REPLY