Wasu mahara da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne sun yiwa kauyen Tabanni dake yankin karamar hukumar Rabah dirar mikiya inda suka kashe dagacin yankin Usman Mohammed tare da halaka wasu karin mutane 45.

Shaidun gani da ido sun tabbatarwa da Daily Nigerian cewar ‘yan ta’addar sun kunnawa kauyen wuta, kana daga bisani suka dinga yin harbin kan mai uwa da wabi ga mutanan da suke gudun ceton rai.

Majiyoyi da dama, ciki har  da dan marigayi dagacin da aka kashe Aliyu Ibrahim sun tabbatar da faruwar wannan lamari, yayin da wasu suke bayyana cewar sun kirga gawarwaki 50 a asibitin Gandi.

“Da farko ‘yan ta’addar sun fara ne da kunnawa kauyen wuta gaba daya, sannan suka koma harbin kan mai uwa da wabi ga mutanen da suke guduwa domin neman tsira da rayukansu yayin da suka ga wuta na ci bal bal”

“Kauyen yanzu ya zama kufai. Mutanan da suka tsallake rijiya da baya a yayin wannan hari suna samun mafaka a kauyen Gandi” A cewar Iro Aminu daya daga cikin mutanan da suka samu tsira yayin da yake shaidawa Daily Nigerian.

Sai dai kuma, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato, Cordeelie Nwawe ya tabbatar da faruwar wannan harin ta’addanci, sai dai kuma yace har yanzu basu kai ga samun alkaluman adadin mutanan da suka rasu ba.

“A halin yanzu an samu nasarar shawo kan lamarin, a saboda haka rundunar ‘yan sanda zata gabatar da sanarwa ta musamman inda zata bayar da bayanai cikakku kan ainihin abinda ya faru” A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan.

LEAVE A REPLY