Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ‘yan syasa da yawa na sukarsa kan batun kashe kashe dake faruwa a Najeriya saboda shi Bafulatani ne.

A Najeriya dai an sha samun rikici tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma a jihohin yankin tsakiyar Najeriya da ya hada da taraba da Binuwai da Nassarawa da kuma Kogi.

An kashe daruruwan rayukan jama’a a sakamakon irin wadannan rikice rikice tsakanin Fulani da manoma.

Sai dai kuma, a lokacin da yake jawabi a yayin gangamin yakin neman zaben Gwamnan jihar Ekiti, Shugaba Muhammadu Buhari yace wasu gurbatattun ‘yan siyasa ne ke sukarsa kan batun kashe kashen saboda shi Bafulatani ne.

 

LEAVE A REPLY