Rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta bayyana cewar ta kama wasu mutum uku da ake zargi da hannu dumu-dumu a kashe kashen da aka yi kauyen Birani dake yankin karamar hukumar mulkin Zurmi a jiharZamfara.

Mutanen da ake zargin su ne: Halilu Garba dan shekara 45 wanda aka fi sani da Mabushi, Zubairu Marafa dan shekara 45 ana kiransa da Wakili, Nafiu Badamasi dan shekara 40 wanda ake kira da sunan Wakili.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewar, maharan, wadan da ake zargin makiyaya ne, a ranar 14 ga watan Fabrairun nan suka kashe mutane 18 a kauyen Birani.

Sifeto janar na rundunar ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya tura runduna ta musamman ta ‘yan sandan kwantar da tarzoma zuwa yankin da abin ya auku.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ta kasa, Jimoh Mashood, ya bayyana cewarmutanan da ake zargin yanzu haka sun fada koma ‘yan sanda, sannan kuma rundunar ta dukufa wajen gudanar da bincike, kuma mutanen suna bada hadin kai.

Mista Mashood ya kara da cewar, daga zarar an kammala bincike za’a mika mutanen kotu domin yi musu Shariah.

NAN ta kuma ruwaito cewar, mataimakin Sufeton ‘yan sanda na kasa, mai lura da sashin bincikena musamman a shalkwatar rundunar ‘yan sandan dake Abuja, tuni ya isa jihar Zamfara ddomin ganin ya taimaka wajen kamo wadannan mahara.

 

NA

LEAVE A REPLY