Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II

 

Hassan Y.A. Malik

‘Yan sanda a jihar Kano sun shelanta cafke wani matashi da yake karyar cewa shi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ne a shafin sada zumunta na Instagram.

Wannan matashi mai shekaru 20, ya yi amfani da marataba da farin jinin Sarki Sanusi, inda har ya tara mabiya fiye da dubu 200 a shafin nasa mai daue da sunan San Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.

Matashin ya samu damar da kamfanin Instagram ya tantance shi ta hanyar ba shi shudiyar alama kuma shafin ya kasance na sirri ne da sai an amince kafin ka fara bin sa duk da cewa yana da alamar tantancewar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano. Magaji Musa Majiya, ya shaidawa manema labarai cewa ana ci gaba da bincike, kuma za su tuhumi mutumin nan ba da jimawa ba da laifin yin sojan gona da kuma zamba.

Ya kara da cewa, Sarkin na daga cikin mutum bakwai da aka yi sojan gona da sunansu, da suka hada da wasu manyan ‘yan kasuwa da manyan masu fada a ji.

‘Yan sanda sun ce mutumin da ake tuhumar ya samu mabiya akalla miliyan uku a dukkan shafukan bogin da ya bude na kafafen sada zumunta.

Ko a watan janairun 2018 ma sai da rundunar ‘yan sandan Abuja, suka kama wata mata da ke yin sojan-gona a matsayin mai dakin shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari.

LEAVE A REPLY