Sufeto janar na rundunar ‘yan sandan Najeriya na sashen binciken leken asiri, IRT, a ranar Asabar ta bayyana cewar, sun ci nasarar ceto wasu Amurkawa biyu da ‘yan Kanada biyu da aka yi garkuwa da su a ranar Talatar da ta wuce a tsakanin Jere zuwa Kagarko a jihar Kaduna.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewar, an kashe ‘yan sanda guda biyu da suke tare da turawan kafin a sace su ayi Garkuwa da su.

Kwamandan da ya jagoranci wannan aiki, Abba Kyari, shi ne ya tabbatar da kubutar da turawan daga hannun mutanan da suka yi garkuwa da su, ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Legas, sannan ya ara da cewar, biyu daga cikin mutanan da suka yi garkuwa da mutanan sun shiga hannu.

Mista Kyari, wanda mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ne, ya bayyana cewar, wata rundunar kwararrun ‘yan sanda ce ta jagoranci wannan aiki da ya kai ga kubutar da mutanen.

“Mun ci nasarar kubutar da AMurkawa biyu tare da ‘yan kasar Kanada biyu, maza uku da mace daya, kuma dukkaninsu suna cikin koshin lafiya, da misalin karfe 7:30 na safiyar ranar Asabar mutanan suka samu ‘yanci”

“Mutanan da aka kubuto da su sune, Nate Vangeest da Rachel Kelley ‘yan Kanada da Amurkawa John Kirlin da kuma Dean Slocum”

“uni aka mika mutanan zuwa ga ofishn jakadancin AMurka dake Abuja domin duba lafiyarsu” A cewar Abba Kyari.

Mutane biyu daga cikin wadan da suka yi garkuwa da mutanan sun shiga hannu, sannan ana kan bincike domin kamo sauran mutanen da suka yi garkuwa da turawan.

NAN

LEAVE A REPLY