‘Yan sanda na neman Kassim Afegbua, mai magana da yawun tsohon Shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida ruwa a jallo kan batun da yayi na cewar kada ‘yan Najeriya su zabi Shugaba Buhari a zaben 2019, inda yace Ibb ne yayi maganar.

Tun a jiya dai ‘yan sanda suka baiwa Kassim Aafegbua sa’o’i 24 da ya bayyana gabansu ko kuma su farauto shi duk inda ya shiga.

A wata sanarwa da Mista Afegbua ya sanyawa hannu, ya ruwaito tsohon Shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida yana cewar kada Shugaba Buhari ya nemi tazarce a 2019.

Sai dai daga bisa, tsohon Shugaban kasa ya nesanta kansa da wadancan kalamai, a wata sanarwa da ya fitar wadda ya sanyawa hannu da kansa.

Haka kuma, ko a daren jiya, Mista Afegbua ya dage akan cewar sanarwar da ya sanyawa hannu tabbatacciya ce daga mai gidansa Ibb inda yace shi ne ya umarce shi da ya fitar  da wannan sanarwar.

Mista Afegbua, wanda ya kasance a matsayin babban bako a wani shiri na musamman da gidan talabijin na Channels yaka gabatarwa a duk ranar Lahadi, yace yana tare da tsohon Shugaban kasa a matsayin mai magana da yawunsa fiye da shekaru 13, yace bai taba fiiar da wata sanarwa da ba umarnin mai gidansa bane.

“Ina yin wannan aiki fiye da shekaru 13, ban taba fitar da wata sanarwa da ta shafi tsohon Shugaban kasa IBB wadda ba shi ya sanya ni ba”

“Sai da na samu sahalewa daga gareshi (Babangida), kafin na bayar da waccan sanarwa. Tsohon Shugaban kasar ya amince da sanarwar da na rubuta kuma na sanyawa hannu, ban yi wannan bayanin a karan kaina ba in ba sanya ni aka yi ba”

Mista Afegbua yace, da yawan abokan arziki na tsohon Shugaban kasa IBB wadan da suke masa makauniyar soyayya, sun yi ta yamadidi da sanarwar farko da na bayar, inda suka dinga tararrabin wannan sanarwa kan Shugaba Buhari.

“Kun san shi IBB na kowa ne, mutane da yawa suna kaunarsa fiye da yadda yake son kansa, mutane suna yaba masa fiye da yadda yake yabawa kansa, mutane da yawa na son kwaikwayon dabi’unsa”

“A lokacin da na fitar da wannan sanarwa, wasu abokansa da suka ga sanarwar a shafukan sada zumunta na intanet tana tayar da kura, sun yi ta tunanin muna neman jefa rayuwar tsohon Shugaban kasa cikin garari ne, shi yasa suka yi gaban kansu suka karyata waccan sanarwa da na bayar”

Sai dai kuma, Mista Afegbua, a wata tattaunawa da yayi da tsohon Shugaban kasa ta wayar tarho, ya tabbatar masa da cewar a fitar da wannan sanarwar da sunansa, kuma abinda aka rubuta din ya yadda ya gamsu cewar kalamansa ne.

“Amma dai bayan fitar wadannan bayanai, nayi magana da shi, ya gaya min cewar kada na damu maganar da na fada daidai ce”

“Tun uni nayi magana da gidajen yada labarai cewar, su yada wannan sanarwa domin babu wata tababa akanta, domin bayani ne wanda shi IBB ya aminta d shi ya kuma bayar da sanarwar a fitar da shi”

Jaridar Guardian ta ruwaito.

LEAVE A REPLY