‘Yan sanda a babban birnin tarayya Abuja, sun yiwa gidan Sanata Dino Melaye dake unguwar Maitama a Abuja kawanya, ‘yan sandan sun kunshi jami’ai na musamman da suke kwance bamabamai, da kuma masu binciken kwakwaf.

Wannan abin ya faru ne ‘yan awanni bayan da aka sallami Melaye daga tsarewar da jami’an hukumar kula da shige da fice na kasa NIS suka yi masa. DIno Melaye dai dan majalisar dattawa ne dake wakiltar jihar Kogi ta yamma a majalisar  dattawa.

An tsare Dino Melaye ne a filin jirgin saman kasa da kasa dake Abuja,akan hanyarsa ta zuwa kasar Moroko, inda ya shafe awa biyu da rabi a hannunsu, jim kadan da fitowarsa daga hannun jami’an ya bayyana soke tafiyarsa zuwa kasar ta Moroko.

A cewar ‘yan sanda, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, cewar, ‘yan sanda sun  yi zaton Melaye ya koma gidansa dake Maitama bayan da ya fito daga ofishin jami’an hukumar kula da shige da fice, inda ya soke tafiyarsa zuwa kasar Moroko.

Haka kuma, anga ‘yan sanda cikin farin kaya suna zazzagawa a kewayen gidan Sanatan dake unguwar Maitama dake Abuja.

Anga ‘yan sanda na rarraba kansu a sassan gida, inda suka ja suka kame, suna yin muzurai a harabar katafaren gidan dake unguwa mafi tsada a babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai kuma, a cewar jaridar Vanguard, Sanata Melaye kamar yasan abinda zai faru a gidansa, dan haka da yafito daga filinn jirgin sama, bai zarce gidansa ba, sai yayi wani wajen daban.

Haka kuma, kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Jimoh Mashood bai samu ba a wayar tarho domin jin ta bakinsa har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Mataimakinsa, Aremu Adediran shima bai dauki wayar da akai ta buga masa ba a wayarsa ta tafi da gidanka.

A hannu daya kuma, magoya bayan Sanata Dino Melaye sun fara yin gangami domin yin maci zuwa gidan Sanatan dake Maitama domin nuna cikakken goyon bayansu a gareshi, da kuma jinjinawa sanatan.

 

LEAVE A REPLY