Daga Hassan Y.A. Malik

Hukumar kididdiga ta kasa NBS, ta fitar da wani rahoto da ya nuna cewa ‘yan Nijeriya 1,306 ne suka mutu ta hanyar hatsarin mota a tsakanin watanni 3 na karshen shekarar 2017.

Rahoton ya nuna cewa daga cikin mutane 1,306 da suka rasa rayukan nasu, mutane 1,200 (kaso 92 cikin 100 na mutanen) sun wuce shekarun balaga, inda ragowar mutane 106 (kaso 8 cikin 100) kuma suke yaran da basu kai shekarun balaga ba.

Haka kuma, mutane 1,019 (kaso 78 cikin 100) na mutanen da suka mutu maza ne, inda ragowar 287 (kaso 22 cikin 100) suke mata.

Rahoton har lau, ya bayyana adadin hadurran da aka samu a tsakanin watan Satumba zuwa Disambar 2017 a matsayin 2,489, kuma kaso 45.8 na  wannan adadi, gudu na fitar hankali ne ya haddasa su.

Tukin ganganci da kuma kwacewar mota daga hannun direba ya dauki kaso 10.8 na adadin hadurran da aka samu a watanni ukun karshe na shekarar 2017.

Adadin hadurran, kamar yadda rahoton na NBS ya nuna, ya ce mutane 7.349 ne suka samu raunika daban-daban daga adadin hadurran da aka samu a wancan tsakani, kuma mutane 6,855 (kaso 93 cikin 100) manya ne da shekarunsu na haihuwa suka shige shekarun balaga, ragowar 494 (kaso 7 cikin 100) suke yara masu kananan shekaru.

Haka kuma dai, cikin wancan adadi na mutanen da suka samu raunika, maza 5,366 (kaso 73 cikin 100) ne, mata kuma 1,983 (kaso 23 cikin 100).

Rahoton ya bayyana adadin mutanen da suka yi lasisin tukin a wancan tsakani da adadinsa ya kai: 214,256. A wannan adadi, jihar Legas da birnin tarayya Abuja ke da mafi yawan mutanen da suka yi lasisin, inda jihohin Zamfara da Kebbi ke da mafi karancin mutanen da suka yi lasisi a watanni uku na karshe na 2017.

LEAVE A REPLY