Hassan Y.A Malik
Mayakan kungiyar Boko Haram sun yi nasarar kashe daya daga cikin kwamandojin sojin Najeriya, Lafatanal Kanal A.E. Mamudu da yammacin yau Alhamis a cikin dajin Sambisa.
Mayakan na noko Haram sun samu wannan nasara ne a yayin da suka dasa bam a motar da jarumin kwamanda ke faturu tare da wani matashin sojan ruwa.
Abokan aiki sun bayyana Lafatanal Kanal Mamudu a matsayin namiji, gwarzon soja, maras tsoro.
Wannan dai shi  ne karo na biyu da hukumar tsaro ta Nijeriya ta ke turo Lafatanal Kanal Mamudu aiki zuwa yankin areawa maso gabas mai cike da fitintinun ‘yan tada kayar baya na Boko Haram.
Ya fara zuwa a shekarar 2015, sai kuma a bara aka sake turo shi a matsayin daya daga cikin kwamandojin atisayen nannauyan naushi.
Marigayi Lafatanal Kanal A.E. Mamudu dan asalin jihar Kogi ne.

LEAVE A REPLY