Daga Jaafar Jaafar

A wata fafatawa da aka yi tsakanin sojojin Nigeria masu yaƙi da ta’addaci a arewa maso gabashin ƙasar da ‘yan ƙungiyar Boko Haram, wani ɗan sanda da wata ‘yar gudun hijira sun rasa rayukansu.

Kakakin Runduna ta Bakwai K.M. Samuel ya ce ranar Juma’ar nan da misalin ƙarfe shida na yamma sojojin su ka yi wa maharan kwanton ɓauna yayin da su ke tsallaka ƙauyen Bocobs da ke ƙaramar hukumar Bama a Jihar Borno.

A cewarsa, nan take sojojin su ka fara yi musu luguden wuta har su ka kashe guda cikinsu kuma su ka raunata da dama.

Bayan sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addar, sojin sun ƙwato kekuna guda uku da jarkoki guda biyar da buhunan masara guda biyu.

Sai dai kuma a wannan rana da misalin ƙarfe bakwai na dare sojojin sun sake artabu da maharan yayin da su ka far ma wani ƙaramin sansanin soji a garin na Bama.

A wannan hari ne aka kashe dan sanda guda daya, kuma harsashi ya samu wata ‘yar gudun hijira ita ma ta mutu.

Kwamandan Birged ta 21 ya ziyarci filin dagar a yau, kuma daga bisani ya zarce a ka yi jana’zar ‘yar gudun hijirar da ta rasu.

LEAVE A REPLY