Daga Hassan Y.A. Malik

‘Yan binga sun kai hari akan babban gidan yari na garin Minna, jihar Neja a yammacin jiya Lahadi, inda suka kubutar da wasu ‘yan busin su 16 da aka riga aka yankewa hukuncin kisa da ma wasu da dama.

Jaridar Daily Nigerian ta gano daga majiya mai tushe cewa ‘yan bindigar sun yi amfani ne da damar mamakon ruwan saman da ya sauka a yankin da gidan yarin ya ke da misalin karfe 7:00 na yammacin jiyan.

Gandirobobin da ke bawa gidan yarin tsaro sun ranta a na kare bayan da suka fuskaci cewa bindigogin ‘yan bindigan sun fi nasu kyau da inganci.

‘Yan bindigan sun kashe wani gandiroba da da dan achaban da ya kawo shi wajen aiki a lokacin da harin ke faruwa.

 Bata kashi tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindigan ya shafe awa guda ana fafatawa har sai da jami’an tsaron suka sake samun dauki daga wata runduna da ta zo don korar ‘yan bindigar, kafin su janye su kama gabansu.

Ko a ranar 6 ga watan Disambar 2014 ma dai sai da akalla ‘yan bursin 300 suka kubuta bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai wa gidan yarin na Minna hari.

Zuwa yanzu dai ‘yan sanda basu ce komai game da harin ba.

Za mu kawo muka karin bayani na gaba…

LEAVE A REPLY