Daga Hassan Abdulmalik

Rahotanni daga jihar Kaduna na nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Sarari da ke kusa da garin Kuriga a Karamar Hukumar Birnin Gwari, inda suka kashe sarkin kauyen da wasu mutane biyar.

Wannan mummunan Lamarin dai ya faru ne a jiya Alhamis.

Harin, wanda ya faru da misalin karfe biyu na rana, ya kuma haifar da jikkatar akalla mutane 8, kamar yadda jaridar Premium Times ta rahoto.

Daya daga cikin wadanda suka jikkata mai suna Henry shi ya tabbatar da mutuwar sarkin kauyen nasu.

Ya ce, “‘Yan bindigar sun faso cikin garin ne yayin da suke harbe-harbe, inda ba su yi wata wata ba suka doshi gidan sarki.”

“Ban san daga inda suka fito ba. Muna zaune ne kawai sai muka fara jin harbi ta ko’ina.”

“Da yawan su suka zo kuma a kan babura. Suna bi gida-gida suna harbin mutane. Sarkin kauyen mu da wasu mutum biyar duk an kashe su. Ni kuma an harbe ni a kafa a lokacin da nake kokarin tserewa,” inji Henry.

Tuni dai aka kai wadanda suka jikkatan asibiti mafi kusa da inda lamarin ya faru.

Karamar hukumar Birnin Gwari dai na shan fama da hare-haren ‘yan bindiga, wadanda ba a tabbata ko su waye ba.

LEAVE A REPLY