A wani hari da ake kyautata zaton na ramuwar gayya ne, ‘yan bindiga dadi da ake kyautata zaton masu biyayya ne ga Buharin Daji sun kashe sojoji 11 a ranar Talata da daddare a yankin karamar hukumar birnin Gwari a jihar Kaduna.

Shaidun gani da ido sun tabbatarwa da majiyar PRNigeria cewar maharan wanda suke shirye sun tasamma wani wajen da sojoji suke a yankin Doka dake tsakanin Funtuwa da Birnin Gwari kuma suka kashe sojojin a wajen.

Tuni aka dauki gawarwakin sojojin zuwa sashin adana gawarwaki da ake kira Mutuware.

Majiyar PRNigeriya tace, tattara wasu alkalu da suke nuna cewar, maharan sun kai hari a yankin Gundumar Maganda da yammacin wannan ranar da zasu kai wannan harin, kuma sun yi ne domin ramuwar gayya akan kisan Buharin Daji da aka yi.

Bayan harin da suka kai a Gundumar Maganda, maharan sun wuce zuwa Kamfanin Doka a wata mahada da take zuwa Gwaska da Dansadau inda nan ma suka kai wani harin da yayi sanadiyar mutuwar wasu sojoji.

Wani jagoran masu sintiri na sa kai, ya shaida cewar, sun sanar da Gwamnatin jihar Kaduna tun makon da ya gabata cewar ana ganin zirga zirgar wasu mutane da ba’a sansu ba a yankin Birnin Gwari zuwa Funtuwa zuwa Dansadau amma babu abinda aka yi.

Shaidar suka tabbatar da cewar, “yayin da aka kashe shugaban ‘yan ta’addar buharin Daji a yankin Nabango dake yankin Birnin gwarikimanin kilo mita 16 zuwa Dansadau a jihar Zamfara, inda nan ne aka samu rahoton ganin wasu mutane da ba’a sansu ba suna shige da fice”

“Mutane sun ce anga wasu bakin fuska dauke da muggan makamai a yankunan Goron Dutse da Kuiga da Maganda da Unguwar Nachibi kuma nan da nan suka kai korafi ga Gwamnatin jihar Kaduna, amma babu wani abu da aka yi”

“Tun bayan kisan da aka yiwa Buharin Daji, masu garkuwa da mutane suke cin karensuu babu babbaka a yankin Birnin-Gwari zuwa Funtuwa a kusan ko da yaushe. Wasu kauyukan dake wannan hanyar an tarwatsa su musamman kauyukan Kirazo da Layin Mai Gwari duk sun tashi sun koma cikin garin birnin Gwari.

“Bayan da rundunar sojan Najeriya ta kaddamar da ‘Operation Karamin-Goro’ a yankin Birnin-gwari duk an janye su daga yankin, inda aka bar wasu sojoji ‘yan kadan a cikin gari”

 

LEAVE A REPLY