Daga Amadu Bauchi

Shugaba Buhari Yayi Sallah idi a Garin Daura Talakawa na kara Nuna Soyayyan su ga Baba Buhari

Shugaba Buhari, Yayi Tafiya Mai Tsawo cikin Talakawan sa Bayan Sallah idi kanda Suke Cigaba da nuna Masa Soyayya da Goyon baya

”Shugaban kasa Muhammadu Buhari,’ ya gudanar da Sallah idin sa a jihar Katsina a garin su na asali wato garin Daura ” Shugaba Buhari, wanda ya samu halartan sallah idi na babban sallah a Masallacin idi na kofar Arewa na garin Daura”

”Shugaban kasa Muhammadu Buhari’ ya isa masallacin ne da wasu daga cikin tawugan sa kanda suka hadu da Mai Martaba Sarkin Daura Alh Farouk Umar Farouk da Magajin Garin Daura Alh. Musa Umar, da Dan Sarkin Daura Yarima Ado Bayero, da babban mai bawa Shugaban kasa shawara akan aiyuka na musamman Alh Yau Darazo, da Matemaki na musamman ga shugaban kasa Tunde Sabiu,da Hon. Musa Daura.

” Bayan idar da Sallah shugaba Buhari, yayi Tattaki a akan kafan sa domun samun Daman ganawa da talakawan sa kanda Buhari, ya shafe tsawon lokaci yana amsa gaisuwan masoya da kuma Magoya bayan sa masu son ganin shi da yi masa fatan Alkhairi.

LEAVE A REPLY