Tsohon Shugaban kasa, Cif Olushegun Obasanjo

Dan majalisar wakilai daga jihar Kaduna, kuma shugaban kwamitin kula da harkokin cikin gida, Jagaba Adam Jagaba, a ranar Laraba ya tona asirin yaddatsohon Shugaban kasa Olushegun Obasanjo ya baiwa ‘yan majalisar tarayyar na lokacin cin hancin Naira 500,000 kowanne domin su tsige kakakin majalisa Ghali Na’Abba.

Adams Jagaba, dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kachia da Kagarko a majalisar wakilai ta tarayyadaga jihar Kaduna. Ya bayyana hakan ne a gaban wata babbar kotu a babban birnin tarayya Abuja dake Lugbe a cigaba da Shariar da ake yiwa Faruk Lawan wanda ake zargi da karbar cin hanci kan batun janye tallafin man fetur a zamanin majalisa ta 7.

Yana bayar da jawabi ne a lokacin da Lauyan dake kare Farouk Lawan, Mike Ozekhome, SAN, ya tambaye shi, kan wannan batu da ya shafi tsohon dan majalisar, yace ‘yan majalisar zartarwa sune suka zo da kudaden cikin zauren majalisa domin toshiyar baki ga ‘yan majalisa dan su tsige kakakin majalisa.

“Na gabatar da wannan kuduri gaban zauren majalisa, ya kuma gabatar da kudaden gaban zauren majalisar”

“Na gabatarwa da majalisa Naira Miliyan hudu da rabi, saboda galibin ‘yan majalisar sun auka cikin wannan batu”

“Na tabbatar wadannan kudade cin hanci ne aka bayar, naga manyan motoci makare da kudade zuwa majalisa domin raba kudin. Kowanne dan majalisa a lokacin an bashi Naira 500,000. ‘Yan majalisa 9 ne suka gabatar da kudaden da aka basu gaban zauren majalisar” A cewar Jagaba Adams Jagaba.

“I believed it was a bribe because I saw trucks coming to distribute the money. It was N500,000 per person. It was nine members that tendered their money as exhibit,” the lawmaker said.

LEAVE A REPLY