Janar Sani Abacha

Yadda tsohon Shugaban kasa Janaral Sani Abacha ya rasu kwana daya kafin shirinsa na darkake Jaridar Punch. Tsohon Shugaban gudanarwar jaridar Ajibola Ogunshola ya bayyana haka.

Mista Ogunshola ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da wata makala a yayin wata tattaunawa da tsohon jakadan Najeriya, Walter Carrington.

An gabatar da wata mukalar ne a yayi kaddamar da wani littafi mai suna”Garkuwa ga raunana” wanda Arese Carrington matar tsohon jakadan Amurka a Najeriya ta rubuta. An gabatar da kaddamar da littafin ne a Legas.

Mista Ogunshola shi ne babban bako mai kaddamarwa, yayi dogon bayani, inda ya bayyanawa mahalarta taron irin gudunmawar da kafafan yada labarai suke bayarwa wajen tabbatuwar demokaradiyya a Najeriya. Musamman irin rawar da suka taka a zamanin Gwamnatin kama karya ta Sani Abacha.

Yayi bayanin yadda aka Gwamnatin Abacha ta so yin amfani da karfin soja da kama karya wajen gain ta rufe Jaridar ta Punch, wadda take sahun gaba gaba wajen yaki da mulkin danniya.

“Daya daga cikin manyan editocin jaridar Mista Babfemi Ojudu, bayan da aka sallamoshi daga gidan kaso, ya bayyana cewar, a lokacin da yake tsare, wani soja da suke aikin lura da shi, ya shaida masa a ranar 7 ga watan Yuni na shekarar 1998, cewar Janar Sani Abacha ya gaba dukkan wasu shirye shirye domin darkake gidan jaridar”

“Amma kwana daya bayan bayyana min wannan kuduri na Janar Abacha akan jaridar Punch, wato ranar 8 ga wata, a rannan Allah ya karbi ransa”

Mista Ogunshola a yayin wannan taro ya nuna irin yadda kafafen yada labarai musamman jaridu yadda suka tsaya kai da fata wajen ganin sun yaki mulkin kama karya irin na soja.

Tsohon Shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha ya mulki Najeriya daga shekarun 1993 zuwa shekarar 1998, shekarar da Allah yayi masa rasuwa.

LEAVE A REPLY