Ranar Alhamis da yamma aka yiwa Marigayi Malam Adamu Chiroma jana’iza a masallacin An-Nur dake babban brnin tarayya Abuja. Jana’izar ta samu halartar mutane da yawa cikinsu har da Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaiedam.

Sauran waan da suka halarci sallar jana’izar sun hada da Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa Abba Kyari da Alhaji Mamman Daura wani na kusa da Shugaban kasa. Sauran sun hada da abokan huldar marigayin da suka hada da Dan masanin Daura Alhaji Sani Zangon Daura.

Marigayi Malam Adamu Vhiroma ya rasu ne a wani asibitin Turkawa dake babban birnin tarayya Abuja. Kafin rasuwarsa yana rike da sarautar Dan iyan Fika tsohon Minista kuma tsohon Gwamnan Babban bankin Najeriya.

LEAVE A REPLY