Sanata Shehu Sani

Bayan da aka cire Shugaban kungiyar Sanatocin Arewa dake majalisar dattawa, Sanata Abdullahi Adamu mai wakiltar Nassarawa ta yamma, inda kuma aka maye gurbinsa da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko daga jihar Sakkwato.

Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani yayi karin haske kan yadda aka ce biri ya lakume kudaden kungiyar har Naira miliyan 70, da kuma yadda suka canja Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Wamakko.

Sanata Sani yace, kimanin Naira miliyan 70 mallakar kungiyar, aka cemusu wai biri a gidan gonar Sanata Abdullahi Adamu ya lakume su.

Cire Sanata Abdullahi Adamu ya faru ne bayan wata wasika da mai jagorantar zaman majalisar ta dattawa Sanata Ike Ekweremadu ya karanta, ‘yan mintoci kadan kafin karkare zaman majalisar na ranar laraba.

Wasikar wadda jami’in hulda da jama’a na kungiyar Sanataocin ya sanyawa hannu, yayi karin haske, inda yace an cire Sanata Abdullahi Adamu ne sabida almundahana da kudade da sauran abubuwa da suke da alaka da zambar kudade.

A lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida Sanata Shehu Sani, yace ba yadda zasu lamunci almundahana da kudin kungiya da ya kai zunzurutun kudi har Naira miliyan 70 mallakar kungiyar.

Yace zancen banza ne ma ace wai biri ya lakume wadannan makudan kudade kuma yayi gaba da su a cikin gidan gona.

“Akwai abubuwan da na sani wanda takwarorina na majalisa ba zasu iya fadi ba, amma ni na iya tarar aradu da ka. Lokacin da muka shigo wannan majalisa ta 8, Sanata Ahmed Lawan ya gabatar da kudi Naira miliyan 70 gaban majalisa”

“Wannan miliyan 70 din, kudi ne da aka tara shi tun majalisa ta 7. An hannata wadannan kudade ga kungiyar Sanatocin Arewa dake majalisa”

“Wannan jita jitar da ake yadawa, wadda ban san asali ko tushenta ba, cewar wai biri ya lakume wadannan kudade a gidan gonar Sanata wanda shi ne Shugaban wannan kungiya ta Sanatocin Arewa, abin dai da mamaki”

“Najeriya na neman zama wata abar dariya, da farko ance, beraye sun kori Shugaban kasa daga cikin ofishinsa, sannan kuma, kwanannan aka ce mana wai maciji ya hadiye Naira miliyan 34, sannan kuma yanzu ace wai biri ya lakume Naira miliyan 70, abin da ban mamaki ainun”

Shi dai Sanata Abdullahi Adamu da ake zargin biri ya warce wadannan kudade a gidan gonarsa yaki yadda yace komai kan batun.

LEAVE A REPLY