Tsohon Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Sanata Ali Modu Sheriff

Daga Hassan Y.A. Malik

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, a jiya Litinin ta tarfa tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff na tsawon awanni a ofishin hukumar na Abuja.

Jami’an hukumar ta EFCC sun yi wa Sheriff tambayoyi da suka hada da yadda aka yi tsohon Sanata kuma tsohon Gwamnan ya samu kudi wuri na gugan wuri har dalar Amurka miliyan 72 ya sayi jirgi malakin kansa kirar G650 Gulfstream bayan ya sauka daga gwamna a shekarar 2011. Sheriff dai har jirage biyu gare shi na kashin kai.

Haka kuma, hukumar na zargin Sheriff da yin zaman dirshan akan kudi dalar Amurka miliyan 200 da gwamantin Goodluck Jonathan ta bashi don ya yi sulhu da mayakan Boko Haram don su tsagaita wuta a shekarar 2014.

Hukumar tana so ta tabbatar ko Sheriff ya mika kudaden ga shugaban wata kasa makwabciyar Nijeriya da a can ne aka shirya batun sulhun ko kuwa bai mika kudaden ga shugaban kasar ba da ake zargi dama abokin Sheriff ne.

Sheriff, a jiyan dai an yi masa tambaya game da kudaden da jam’iyyar PDP ta raba a lokacin zaben shekarar 2015 wanda EFCC ta ke so tabbatar ko Sheriff din ya amfana da wadannan kudade.

EFCC, a ranar 6 ga watan Yunin 2016 ta gurfanar da shugaban kamfe na jam’iyyar PDP reshen jihar Borno, Muhammad Wakil, inda Wakil din ya bayyana yadda ya kasafta Naira miliyan 450 din da aka bashi ga wasu jigogin jam’iyyar don gabatar da yakin neman zaben.

Wakil ya bayyana cewa ya raba kudaden ga: Nicholas Msheliya, Peter Biye, Honarabul Kudla Satumaria, Honarabul Ibrahim Birma, dukkanninsu daga kudancin Borno sun samu Naira miliayan 112.34

Sai Honarabul Kangar, ta hannun Dakta Kulima A.A da ya karbi Naira miliyan 88.62. Injiniya Muhammed Baba Kachalla, Honarabul Kaamuna Khadi, Honarabul Zarma Mustapha da Honarabul Abdulrahman Tarab da suka raba miliyan 140.86.

A bayanin da Wakil ya bawa hukumar EFCC, ya bayyana cewa ya mikawa Sheriff Naira miliyan 40 ta hannun Honarabul Kumalia.

EFCC ta saki Sheriff din a jiya a tsarin beli, amma za ta ci gaba da yi masa tambayoyi a yau Talata.

LEAVE A REPLY