Audu Katagum

Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar ya zabi Audu Katagum, Shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin jihar a matsayin sabon mataimakin Gwamnan jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar Umar Sade ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, wannan batu.

Idan za’a iya unawa, a kwanakin baya ne dai tsohon Mataimakin Gwamnan Bauchi, Nuhu Gidado yayi murabus daga mukaminsa, abinda ya haifar da gibi a cikin Gwamnatin.

Tuni dai majalisar dokokin jihar ta karbi sunan Audu Katagum domin amincewa da shi a matsayin sabon mataimakin Gwamnan jihar Bauchi.

LEAVE A REPLY