Tsohowar mai dakin Nelson Mandela, Madam Winine Mandela

Nomzamo Winifred Madikizela-Mandela tsohuwar ‘yar gwagwarmayar kwatar ‘yancinbakaken fata a kasar Afurka ta kudu, kuma tsohuwar mai dakin fitaccen dan gwagwarmayar kasar Nelson Mandela.

Zodwa Zwane babban hadiminta, shi ne ya bayar da sanarwar mutuwarta a ranar Litinin da hantsi, inda yace,  iyalanta zasu bayar da sanarwa nan gaba a hukumance.

An haifi Winnie ne a kauyen Bizana dake gabashin birnin Cape a shekarar 1936, daga bisani ta koma birnin Johannesburg inda ta yi karatun ta a can.

Ta hadu da wani matashi dan rajin kare hakkin bakaken fata da yaki da nuna wariyar launin fata, kuma lauya mai sunan Nelson Mandela a shekarar 1957, sun yi aure shekara guda bayan haduwarsu, sun kuma haifi yara guda biyu tare.

Sai dai aurensu ya lalace ne tun lokacin da aka kama Nelson Mandela a shekarar 1963 inda aka yanke masa daurin zaman gidan kurkuku na har abada. Daga bisani a cikin shekarar 1990 an saaki mandela.

Jaridar Sunday Times, ta ruwaito cewar, lokacin da mandela yake gidan kurkuku, mai dakin nasa an haramta mata yin gwagwarmayar wariyar launin fata, inda aka yi mata kulle a cikin gida.

 

LEAVE A REPLY