Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Wani sanata mai wakiltar Kudancin jihar Taraba a majalisar dattawan Najeriya, Emmanuel Bwacha, a ranar Talata yayi kaca kaaca da Gwamnatin tarayya da aniyarta na bude iyakokin Najeriya a lokacin da ake tsaka da yaki da ‘yan ta’adda, yace wannan batu zai sanya ‘yan ta’adda ketarowa Najeriya.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewar Mista Emmanuel Bwacha, wanda shi ne mataimakin Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Mararraba, da yake maida martani kan wannan batu na Gwamnati.

Ya zargi Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, inda yace bude iyakokin Najeriya zai sanya ‘yan ta’adda daga kasashen Libiya da Chadi da Nijar su shigo Najeriya ba tare da wata matsala ba dan su tayar da tarzoma.

“Ban san dalilin da ya sanya Gwamnati ta kuduri aniyar bude iyakokin Najeriya ba, ko dan a baiwa ‘yan ta’adda dama daga Libiya da Chadi da Nijar su shigo mana ne, domin kashe mana mutane?”

“Ya zama tilas Gwamnati ta farka daga wannan dogon baccin da take yi ta san abinda ya kamata ta yi kan wannan batu” A cewar Sanata Bwacha.

A yunkurin ta na yiwa ‘yan kungiyar Boko Haram afuwa, yace wannan tsabar rashin tunani ne, ace mutanan da suka dauki makamai akan Gwamnati wai kuma wannan Gwamnatin ce zata yi musu afuwa, wato ana son a kara karfafawa ‘yan ta’adda guiwa, su yi abinda suka ga dama, domin sun san za’a yi musu afuwa”

“Na gayawa Shugaban kasa cewar, ni sam ban gamsu da wannan yunkuri da Gwamnati take shirin yi ba, sabida ‘yan ta’addan da aka kama kae tsare da su, ana sakinsu da sunan yiwa ‘yan ta’adda afuwa, wannan sam bai dace ba”

 

LEAVE A REPLY